Dakta Bashir Aliyu Sallau

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Matsayin Sana'o'in Gargajiya na Hausawa Jiya da Yau: Ƙalubale ga Matasan Wannan Zamani


Bashir Aliyu Sallau, Ph.D.
(Sarkin Askar Yariman Katsina Hakimin Safana)
Babban Darektan Hukumar Binciken Tarihi da Kyautata Al'adu
Jihar Katsina – Tarayyar Nijeriya
Kuma
Ɗangaladiman Farfesan Al'adun Hausawa
Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya
Jami'ar Umaru Musa Yar'adua Katsina

Takardar da za a Gabatar a Babban Taron Al'adun Hausa na Ƙasa da Ƙasa (FESTICHA, INTHACFEST, TAHAKA) a Ouagadougou – Burkina Faso Daga Ranar 07 Zuwa 11 ga Watan Disamba, 2018


Tsakure

Tun shekaru aru-aru da suka gabata kafin shigowar Turawa ƙasar Hausa mutanen wannan ƙasa suna da ingantattun hanyoyin da ke taimaka wa tattalin arzikinsu domin dogaro da kai, waɗanda suka haɗa da noma da kiwo da fatauci da sana’o’in gargajiya irin su ƙira da dukanci da rini da saƙa da sassaƙa da jima da wanzanci da fawa da ɗori da sauransu. Tarihi ya bayyana cewa, al’ummar Hausawa mutane ne masu ƙwazo da ƙoƙarin yin ayyukan da za su taimaka wa rayuwarsu yadda za su zama masu dogaro da kai. Wannan dalili ne ya sa a kowane gida da mutum ya ziyarta a ƙasar Hausa, zai tarar mutanen gidan na yin ɗaya daga cikin waɗannan sana’o’i da aka ambata a sama. A wancan zamani za a tarar matasa ne a gaba-gaba wajen tafiyar da waɗannan sana’o’i a inda za a tarar wasu sun mallaki masana’antu na gargajiya don sarrafa kayayyaki daban-daban waɗanda suke sayarwa a kasuwanni na cikin gida ga masu sayen ɗai-ɗaya da kuma masu yin sari don kaiwa kasuwannin da ke maƙwabtaka da ƙasar Hausa na kusa da na nesa. Haka kuma, za a tarar wasu daga cikin waɗannan matasa an ɗauke su domin yin ƙodago a ire-iren waɗannan masana’antu. Shigowar Turawa ƙasar Hausa a cikin ƙarni na 19 da kuma farkon ƙarni na 20 wanda ya haifar da samuwar ilimin zamani (boko) ya kawo babban sauyi wanda ya shafi yadda ake tafiyar da waɗannan sana’o’in gargajiya na Hausawa, don kuwa matasan ƙasar Hausa sun yi watsi da waɗannan sana’o’i suka mayar da hankali wajen samun aikin gwamnati ko na kamfanoni waɗanda Turawa suka kawo a ƙasar Hausa. Yau da kullum ana samun ƙaruwar matasa waɗanda suka kammala karatun sakandare da na gaba da sakandare da ma na Jami’a, sai yawansu ya riƙa ƙaruwa sosai wanda ya haifar da cikowar masu neman aiki a ma’aikatu da hukumomin gwamnati da ma kamfanoni.Wannan ya sa matasa masu yawan gaske duk da suna da ilimin zamani suka rasa wuraren da za su sami aikin da za su yi. Saboda haka ne, wannan takarda za ta yi tsokaci ne kan sana’o’in gargajiya na Hausawa dangane da yadda matasan ƙasar Hausa suka yi watsi da su suka taɓarɓare yadda a wannan zamani har wasu na neman mutuwa a manta da su.

Latsa nan ka Juyi Takarda


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub